Ƙalubalen Tsaro a Masarautar Gummi: Sigoginsa da Dabarun Tunkararsa

  Tsakure

  Matsalar tsaro a yau ta zama tamkar wutar daji da ta buwayi a kashe musamman a Arewacin Nijeriya da sauran sassan ƙasar nan. Jihar Zamfara ta zamo ɗaya daga cikin jihohin da suke fuskantar irin waɗannan matsaloli na tsaro. Galibi yankunan da wannan matsala ta yawaita kuwa sun haɗa da Zurmi, Shinkafi, Tsafe, Maru, Maradun, Talata Mafara, Bakura, Anka, Bukkuyum da kuma Gummi. Wannan muƙala an gina ta ne da nufin nazartar irin ƙalubalen tsaro a masarautar Gummi ta jihar Zamfara da zimmar fito da irin yankunan da suke fama da taɓarɓarewar tsaron da kuma irin ɓarnar da ake yi wa jamaar da nufin samar da wasu dabaru ko hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar tsaron ko magance ta kwata-kwata. A ƙoƙarin tabbatar da binciken an lura da nauoin taaddancin da ake yi wa mutanen yankin kama da satar shanu da garkuwa da mutane da uwa uba kashin gilla na babu gaira babu sabar. An yi amfani da hanyar hirarraki da waɗanda abin ya shafa domin tace bayanan da aka samu a wajen su.

  Fitilun Kalmomi: Tsaro, Masarautar Gummi, Zaman Lafiya

  DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.013

  author/Sarkin Gulbi, A. & Musa, S.

  journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 |  P. 118-124

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1_ceTBeb4YnIy0EXVBTkyBfdRiJ8AGtbD/view?usp=share_link

  paper-https://drive.google.com/file/d/1_ceTBeb4YnIy0EXVBTkyBfdRiJ8AGtbD/view?usp=share_link