Tsakure
Mafi yawan jaridun ƙasar nan sukan buga labaran da suka shafi tsaro a jihar
zamfara amma ba kasafai akan fito da irin waɗannan rahotanni ta fuskar nazari ba. Dalilin wannan bincike shi ne, domin a
cike wani giɓi da aka bari
danagane da tattaro irin waɗannan rahotanni da
suka shafi tsaro daga Jaridar Hausa ta Aminiya. A wannan maƙala, an yi amfani
da hanyar gudanar da bincike ta hanyar ziyartar ofishin jaridar Aminiya da ke Kano da Kaduna, a inda aka yi nazari a kan jaridun Aminiya na Hausa, sannan an ziyarci ɗakunan karatu, inda aka duba bugaggun littattafai da ƙamus-ƙamus da kundayen bincike da mujallu da kuma maƙalun da masana
suka gabatar, musamman waɗanda suka shafi tsaro a jihar Zamfara. Haka kuma, an yi
hira da masana da ma ƙwararru a harkokin tsaro da aikin jarida a kan abin da ya
shafi tsaro a jihar zamfara. Wannan bincike ya
yi duba ne a kan irin rahotannin da shahararriyar Jaridar nan ta Hausa
(Aminiya) take kawowa dangane da abin da ya shafi tashintashinar da ake fama da
ita a jihar Zamfara da ke yankin Arewacin Nijeriya daga shekarar 2015-2019. A
cikin waɗannan rahotanni an
gano yadda masana da malamai da sarakuna da hukumomi da ƙungiyoyi da kuma
sauran al’ummomi suka rinƙa bayar da shawarwari ga gwamnatoci don shawo kan
matsalar tsaro tun tana cikin zanen goyo kafin ta gagari Kundila. A ƙarshen wannan maƙala an bayar da
shawarwari a kan irin matakan da ya kamata a bi don ganin an magance wannan
matsala ta tsaro.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.025
author/Bashir, A. & Umar, M.A.
journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 | P. 226-234
pdf-https://drive.google.com/file/d/1TxolgrqbJJMAzKswXvDQhsVgaaylbNku/view?usp=share_link
paper-https://drive.google.com/file/d/1TxolgrqbJJMAzKswXvDQhsVgaaylbNku/view?usp=share_link