Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta Ga Tashintashinar Zamfara

  Tsakure

  A yau, kafafen sada zumunta sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma, musamman matasa. Suna da tasiri (mai kyau ko marar kyau ko duka biyu) a ɓangarorin rayuwa daban-daban da suka haɗa da zamantakewa da kasuwanci da ilmi da sana’o’i da mulki da shugabanci da makamantansu. La’akari da haka ne ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin haska fitilarsa domin ƙyallaro ko kafafen na da tasiri a kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara? Idan suna da , yaya nauin tasirin yake? Binciken na da manufar (i) bitar yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da (ii) nazartar tasirin kafafen sada zumunta kan waɗannan tashe-tashen hankula. Kasancewar Zamfara ɗaya daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa masu tsohon tarihi. Binciken ya yi amfani da Bahaushen ra’i domin jan akalarsa. An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe mai cewa: “kowane allazi da nasa amanu.” An bi manyan hanyoyi guda biyu domin tattara bayanai. Na farko shi ne hira da aka yi domin samun bayanan nau’ukan tashe-tashen hankulan daga tushe (ganau ko jiyau daga ganau). Na biyu kuwa, an bibiyi kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa na yanar gizo (intanet) domin ganin wainar da ake toyawa dangane da batun da ake magana kansa, tare da tattarowa da nazartar bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubuce da suka shafi manufar binciken. Binciken ya gano cewa, duk da ɗimbin amfanin kafafen sada zumunta, suna taka rawa kai tsaye ko a kaikaice wajen ruruta wutar tashe-tashen hankular jahar Zamfara. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga hukomomi da su fara tunanin yin wata huɓɓasa na bibiya da jagorancin al’amuran kafafen sada zumunta.

  Fitilun Kalmomi: Zamfara, Kafafen Sada Zumunta, Tashe-Tashen Hankula

  DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.011

  author/Abu-Ubaida SANI et al.

  journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 |  P. 95-107

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1FpN3AWIL4CoJx0lRJS1haUXEkQIp2OPh/view?usp=share_link

  paper-https://drive.google.com/file/d/1FpN3AWIL4CoJx0lRJS1haUXEkQIp2OPh/view?usp=share_link