Tsarin Zumuntar Bahaushe Maganaɗison Tsaron Ƙasar Hausa

    Tsakure

    A shekarun baya ƙasar Hausa tana da aminci da tsaro. Tsaron da Hausawa ke da shi na da nasaba da tsarin zumuntarsu. A baya-bayanan nan kuwa, al’amarin tsaro a ƙasar Huasa na fuskantar ƙalubalen ƙara taɓarɓarewa. Wannan takarda ta mayar da hankali wajen nazartar alaƙar taɓarɓarewar tsaro da tsarin zumuntar Bahaushe a yau. A matsayin dabarar gudanar da bincike, an nazarci jaridu tare da bibiyar kafafen watsa labarai da na sada zumunta. Bugu da ƙari, an bi diddigin waɗansu ayyukan ta’addanci har zuwa wuraren da suka wakana domin samun bayanai daga tushe. Sakamakon binciken ya yi daidai da hasashensa inda ya bayyana akwai alaƙa ta kai tsaye da ta kaikaice tsakanin tsaro da tsarin zamantakewa. A fahimtar wannan bincike, lamarin inganta tsaro ya kasance tamkar kurar gardi. Tabbatar da tsaro da zaman lafiya na buƙatar saka hannun dukkannin ɓangarorin al’umma tun daga kan jami’an gwamnati, shuwagabanni, har zuwa kan ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun al’umma.

    Fitilun Kalmomi: Tsaro, Zaman Lafiya, Tsarin Zumunta, Hausawa

    DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.010

    author/Aliyu Muhammad Bunza

    journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 |  P. 86-94

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1H_X6VY9f10Jm435jiyIa6TYwyS47iSeL/view?usp=share_link

    paper-https://drive.google.com/file/d/1H_X6VY9f10Jm435jiyIa6TYwyS47iSeL/view?usp=share_link