Bauɗaɗɗiyar Ɗabi’a a Habarcen Hausa: Nazari Daga Wasu Tatsuniyoyin Hausa

  Tsakure

  Ɗabi’a hali ne da ake iya hango shi a tattare da tauraro a cikin habarcen tatsuniya, wannan ɗabi’a tana iya kasance wa bauɗaɗɗiya ko kuma akasin haka, ma’ana hakan ya danganta da yadda mawari ya tsara taurarinsa a cikin habarcensa na tatsuniya. Kowace irin ɗabi’a mai kyau ko akasinta tana da alfanu ga tauraro wajen sakamako. Nazarin ya tattake wajen iya kalato ɗabi’u bauɗaɗɗu waɗanda mawari ya yi amfani da taurarinsa wajen fayyace ɗabi’un cikin habarcen tatsuniya. Haka kuma nazarin ya fito da yadda taurari ke baje kolinsu wajen gudanar da rayuwa ta baɗini da irin waɗannan halaye bauɗaɗɗu. Har ila yau, an iya samun haka ne ta hanyar tattara bayanan tatsuniya daga cikin littatafai waɗanda kusan su ne ginshiƙan wannan bincike da kuma tsefe su tunya-bunya a wannan muƙala, domin masu nazari su fahimci hanyoyi ko matakan da aka bi wajen ƙalailaice bayani tare da misalai.

  Fitilun Kalmomi: Ɗabi’a, Tatsuniya, Hausa, Adabi

  DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.016

  author/Muhammad Rabiu TAHIR

  journal/Tasambo JLLC | 15 May 2023 |  P. 131-137

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1uJIhjCihck1wXje7WKher16xdk_Y47dg/view?usp=share_link

  paper-https://drive.google.com/file/d/1uJIhjCihck1wXje7WKher16xdk_Y47dg/view?usp=share_link