Tsakure
A ƙasar Hausa, masu aiwatar da sana’o’in gargajiya suna da muhimmanci matuƙa. Baya ga samar da kayayyakinsu ga masu saya, suna kuma taimakawa sosai ga sha’anin bayar da magungunan gargajiya. Kowane mai sana’ar gargajiya yana da fannin da ya ƙware a sha’anin magani. Manoma, ga misali, su suke bayar da maganin ciwon baya da na zafin rana. Sarkawa, waɗanda sana’arsu ita ce kamun kifi, na da muhimmanci matuƙa wajen samar da kifi, wanda ke ɗauke da sinadarai masu gina jiki da ƙara lafiya. Baya ga wannan suna gudanar da muhimmin aiki dangane da abin da ya shafi bayar da magungunan gargajiya. Waɗannan ayyuka nasu na bayar da maganin gargajiya ne wannan muƙala ta ƙuduri warware zare da abawarsa. Binciken an aiwatar da shi ne ta hanyar bibiyar Sarkawa tare da yin hira da su domin zaƙulo ire-iren gudumawar da suke bayarwa a fagen kiwon lafiya.. Muƙalar, ta gano cewa suna bayar da magunguna na waraka daga cutar sanyi da ma sauran cututukan da ake iya ɗauka a cikin ruwa kamar tsagiya da cutar ƙaiƙayin jiki da cutar sanyi. Haka kuma suna bayar da magungunan riga-kafi, da magungunan biyan buƙatun zuciya, har ma da na siddabaru, da na sharri. Muƙalar ta karkata ga magungunan cututukan jiki, waɗanda Sarkawa suke taimaka wa al’umma da su. Yana da kyau masana ilimin haɗa magunguna na zamani su yi ƙoƙarin gano sinadaran da ke ƙunshe cikin magungunan da sarkawa suke bayarwa da nufin ƙara inganta su da kuma zamanantar da su.Yin haka zai taimaka wajen samar da kiwon lafiya mai rahusa ga al’umma.
Fitattun Kalmomi: Tsakure, Gudunmuwa, Sarkawa, Kiwon lafiya, Gargajiya