Nazari A Kan Hausar ‘Yan Lakum A Garin Gusau Na Jihar Zamfara

    Tsakure

    Wannnan muƙala ta cike gurbin da aka bari na nazarin ilimin walwalar harshe, duk da cewa manazarta da masu bincike sun yi bincike a kan Hausar rukunin jama’a daban-daban amma ba a ci karo da wadda ta yi magana a kan Hausar ‘yan lakum ba. Saboda haka wannan binciken ya yi ƙoƙarin zaƙulu ko fito da kalmomi da jumlolin da ‘Yan lakum ke anfani da su yayin sadarwa a tsakaninsu. Sannan ya gano hanyoyin da suke bi domin samar da kalmomi nasu. Yayin gudanar da wannan bincike an yi amfani da fitattu kuma sanannun hanyoyin gudanar da bincike da suka haɗa da: Bitar ayyukan da suka gabata, Hira ko zantawa da masu wannan harka, Ziyartar hafukan yanar-gizo, da kuma Sa-ido ko lura (observation). An ɗora wannan aiki a kan Ra’in fage (field theory) na Lehrer (1969). Akan yi amfani da wannan Ra’i ne domin fayyace irin canje-canjen da ake samu a cikin harshe, da yadda ma’anar kalma kan iya canzawa gaba ɗaya daga ma’anar da aka san ta ita tun da farko.

    Fitilun Kalmomi: Hausar Rukuni, Walwalar Harshe, ‘Yan Lakum

    DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.014

    author/Abdullahi Bashir & Sabitu Sani

    journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 124-133

    pdf-https://drive.google.com/file/d/10kJSpy5gfWgsGBU3vMp92II1Q8ollfc4/view?usp=sharing

    paper-https://drive.google.com/file/d/10kJSpy5gfWgsGBU3vMp92II1Q8ollfc4/view?usp=sharing