Tsakure
Harshe yana samun sauye-sauye ta hanyar bunƙasa da faɗaɗa da kuma samun baƙin al’amurra cikinsa da sukan faru lokaci-lokaci. Wannan maƙala mai taken ‘Nazarin Ƙirƙira da Ma’anar Wasu Sunayen ‘Yan Ta’adda ta Hanyar Aro da Kwaskwarima a Arewa Maso Yammacin Nijeriya’ maƙala ce da ta yi nazarin bunƙasar harshen Hausa da aka samu dalilin ayyukan masu ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Maƙalar ta yi ƙoƙarin fitowa da wasu sababbin sunayen da ‘yan ta’adda suke kiran kansu da su waɗanda suka ƙirƙira wa kansu domin amfani da su wajen sadarwarsu ta yau da kullum da kuma wasu sunaye da mutane suke kiran su da su. Manufar maƙalar ita ce, tabbatar da bunƙasar da harshen Hausa ya samu a dalilin ayyukan ‘yan ta’adda ta hanyar samar da ƙirƙirarrin sunaye na gama-gari da ake kiran su da su da kuma sunayen da suke laƙaba wa kansu da kuma sunayen da ake yi masu. An yi amfani da ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ (Language of Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008), wajen gudanar da wannan bincike wanda yake magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da waɗanda ke yaƙar su. Ra’in ya nuna cewa, idan aka yi la’akari da kalmomin da ɓangarorin biyu ke furtawa, to akwai abubuwan da ake samarwa dangane da harshe da bunƙasarsa. Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da aka rubuta wannan maƙalar akwai; tattaunawa da ‘yan ta’adda da suka tuba da mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, amma daga baya suka samu ‘yanci, da ‘yan jarida da wasu ɗaiɗaikun mutane da ayyukan ta’addanci suke aukawa a cikin yankunansu. Haka kuma, an yi amfani da sunayen da ake ji na ‘yan ta’adda a kafafen sadarwa da kuma kafafen rediyo da talabijin da jaridu da mujallu na intanet.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.028
author/Sarkin Fada, I. & Abdullahi, M.
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 28