Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga Jumla Maras Aikaitau

    Tsakure

    Hausa da Fulatanci harsuna ne mabambanta ta fuskar tarihin tushensu da kuma nahawu. Duk da haka, ba a rasa wuraren da suka yi kama da juna ta fuskar jumlolinsu ba. Manufar wannan muƙala ita ce ƙoƙarin kwatanta korewa a jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci domin a fito da kamancinsu da kuma bambancinsu ta fuskar gininsu. Hakan zai samu ne ta yin la’akari da ire-iren waɗannan jumloli a harsunan Hausa da Fulatanci. An yi amfani da hanyar hira daga wasu rukunin Hausawa da Fulani tare da nazartar littattafan nahawu na harsunan guda biyu wajen tattara bayanai a wannan bincike. Sannan mai gudanar binciken ta yi amfani da kasancewarta mai jin Fulatanci kuma manazarciyar harshen Hausa wajen ƙalailaice bayanan da ta samu waɗanda suka kai ga samar da sakamakon wannan bincike. Haka kuma, an ɗaura aikin a kan ra’in ɗoriya na Haliday. A wannan muƙala, an kwatanta ire-iren jumloli waɗanda suka haɗa da jumla ganau da jumla ƙaddamau da kuma jumla rayau. An gano cewa akwai kamanci musamman ta fuskar adadin kalmomin korewa da kuma yadda ake sarrafa su a jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci. Bugu da ƙari, an gano bambanci a tsakanin jumla korau ta fuskar kalmomin da suke yin tarayya da ɓurɓushin korewa wajen isar da saƙo.

     DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.029

    author/Usman Muhammad, PhD 

    journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 29