Nazarin Kurman Ɗa a Waƙar “Zuma” Ta Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    Tsakure

    Takardar ta yi nazarin waƙar baka ta ALA inda aka bibiyi amfani da ‘Kurman Ɗa’ wanda shi ne ya mamaye waƙar ‘zuma’ ta mawaƙin. An fahimci yadda ya yi amfani da hikima da azanci domin isar da saƙonsa ga masu nazari. ALA ya yi ta faman dibilwa ta amfani da harshen Hausa, wadda sai da manazarta suka ci kwakwa kafin fahimtar saƙon mawaƙin a cikin sauƙi. Dalilin wannan nazari domin masu sauraron waƙa da manazarta sun gaza yin caraf! Domin fahimtar saƙon da ke cikinta, sakamakon haka sai aka nazarce ta, aka fahimce ta, aka kuma tattauna da mawaƙin, sannan aka yi fashin baƙinta, domin fahimtar da ɗimbin masu gurguwar fahimta game da waƙar. Tunanin rubuta wannan takarada bai wuce fitar da jaki daga duma ba, domin salon sarƙaƙiyar da saƙon waƙar yake da shi. An saurari wannan waƙa ne a cikin faifan memory, sai aka rubuce ta tsaf domin yin wannan nazarin. Manufar wannan takarda ita ce fahimtar yadda mawaƙin ya nuna ƙwarewa ta amfani da harshe, domin kuwa takardar ta binciko yadda manazarta da dama suka wasa ƙwaƙwalensu domin gano haƙiƙanin saƙon da waƙar take ƙunshe da shi, sakamakon yadda saƙon ya dinga zuwa a dunƙule kuma cikin salon tambaya tare da salon waskiya daga mawaƙin, har dai daga bisani a ka fahimci bakin ƙullin zaren ta yadda mawaƙin ya yi amfani da salo irin na ɗaurin ɓoye.

     DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.024

    author/Murtala Garba Yakasai Ph.D.

    journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 24