Tsakure
Waƙa na
ɗaukar kaso mai tsoka daga cikin adabin
Hausa, wadda kusan babu wani rukuni ko fagen adabi da ba ta ratsawa walau na baka
ne ko rubutacce. Waƙa
Hanya ce ta isar da saƙo
cikin hikima da azanci gami da sarrafa harshe cikin rauji. Masana sun tabbatar
da cewa kafin Bahaushe ya mu’amalanci Larabawa ya koyi rubutu da karatu yana
aiwatar da waƙarsa
ne da baki ya adana abarsa a ka. Daga bisani ya fara rubuta ta ta hanyar amfani
da ƙa’idoji da tsari irin na waƙoƙin
Larabawa kasancewar daga gare su ya fara samun iliminta. Samuwar ilimi a wurin
Bahaushe (musamman na rubutu) tare da cuɗanya da adabin Larabci ya haifar masa da
samuwar rubutacciyar waƙa,
wanda kafin wannan lokacin ba shi da ita. Daga nan ne aka iya samun nau’o’in waƙa iri biyu, watau ta baka da rubutacciya
ko kuma waƙa 1
da waƙa 11 kamar yadda Muhammad (1973 da 1981)
ya kira su, kuma kowace tana da tsarinta da kuma sigoginta. Bayan lokaci mai
tsawo a farko farkon wannan ƙarni
da muke ciki (Ƙarni
na ashirin da ɗaya), Hausawa sun sami ɓullowar
wata nau’in waƙa wadda
ita ba za a kira ta kai tsaye da ta baka ba, haka kuma ba za a kira ta
rubutacciya ba,
domin kuwa ta sha bamban da dukka guda biyun ta fuskar aiwatar da ita da
tsarinta da kayan kiɗanta da kuma hanyar adana ta. Wannan maƙala ta yi ƙoƙrin
bibiyar wannan nau’in waƙa ne
tare da duba yadda masana suka ɗauke ta da ƙoƙarin
gano matsayinta a wurin ɗalibai da manazarta da kuma kallon ta a
matsayin wani kaso na waƙa
mai cin gashin kanta. Maƙalar
ta tattara bayanan da ta yi amfani da su ne ta hanyar tattaunawa da masana a
wannan fage tare da ƙwararru
waɗanda su ke aiwatar da ita wannan nau’in
waƙar. Haka kuma ta bibiyi yadda masana
suka ƙwanƙwance
kowace nau’in waƙa
tare da kallon abubuwan da suka bambanta nau’o’in waƙoƙin,
tare da kallon matsayin da suka ba ita wannan waƙa. A
ƙarshe maƙalar
tana ganin akwai buƙatar
masana da manazarta su sake duba wannan nau’i na waƙa (waƙar ƙarni na ashirin da ɗaya),
sannan su kalle ta a matsayin wani kaso mai zaman kansa daga cikin rabe- raben
waƙa (waƙa
III), domin kuwa tana da wasu sigogi nata waɗanda suka bambanta ta da sauran nau’o’in
waƙa guda biyu da ake da su (Waƙar baka ‘waƙa I’ da Rubutacciyar waƙa ‘Waƙa
II’).
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.044
author/Rabiu Bashir PhD
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 44