Tsakure
An gina
wannan maƙala ta yin la’akari da wasu waƙoƙi biyu na
marubuta biyu a kan wasu fari da suka addabi al’umma a cikin ƙauyuka da
birane ta hanyar cin hatsin da aka noma tare da nakasa shi tun yana tsaye. An
lura da wasu abubuwa da marubutan suka yi canjaras da juna a cikin waƙoƙinsu, duk da
yake babu wanda ya tuntuɓi wani kafin ya rubuta ko lokacin da yake rubuta waƙarsa.
Abubuwan da aka yi kwatance tsakanin waƙoƙin biyu sun
haɗa da mabuɗin waƙoƙin da
marufinsu da saƙon waƙoƙin
kasancewarsu iri ɗaya, na tarihi. Bayan haka an kwatanta waƙoƙin ta fuskar ambaton sanadiyyar zuwan farin da kuma
ayyukan da suka yi na cutar da
al’umma. Haka kuma marubutan sun ambaci farin dukkansu da rashin jin kora bayan
sun sauka bisa hatsi. Ba
wannan kaɗai ba,
marubutan sun ambaci farin sun yi zagayen garuruwa da yawa, wanda ke nuna ba wuri ɗaya suka
tsaya da ayyukansu ba. Kwatanta waƙoƙin biyu da aka yi, marubutan sun faɗi lokacin
zuwan farin babu bambanci, wato duk a lokaci ɗaya suka zo
ko cikin shekara ɗaya. Dangane da yawan layukan da suka zuba a
matsayin baiti duk tangam (iri ɗaya) ne. Kowannensu ya samar da
baitin waƙarsa ta hanyar shirya shi da
layuka biyu kacal (‘yar tagwai ce). Tare da haka, duk abubuwan da aka ambata na
kwatance tsakanin waƙoƙin marubutan biyu an raka su da misalan da mai
karatu zai fahimci inda maƙalar ta dosa.
Haka na tabbatar wa mai karatu cewa, kwatancen da aka yi da misalan da aka kawo
na tabbatar da waƙoƙin sun mallaki wasu siffofi iri ɗaya da ake
samu a cikin kowaccensu.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.043
author/Dano Balarabe Bunza (PhD)
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 43