Gurbin Adawa a Siyasar Zamani

     Tsakure

    Salon mulkin siyasa wani tsari ne da al’umma suke zaɓen wakilansu da kansu bisa ga cancantar ɗan takara da kundin tsarin mulki ya yarda da shi. Wato, siyasa wani salon mulki ne na farar hula da ke bai wa ‘yan ƙasa yanci da damar saka kansu a dama da su a shaanin mulki. Wannan bincike mai taken Gurbin Adawa A Siyasar Zamani, bincike ne da ya shafi gudummawar da adawa take bayarwa wajen kawo sauyin salon tafiyar da shugabanci, ta hanyar haska wa masu mulki kurakuransu domin su gyara da kuma yi musu hannunka-mai-sanda ko gargaɗi ga yadda ya kamata su aiwatar da abubuwan da za su amfani al’ummar da suka zaɓe su. A wani ɓangare kuma adawa tana ilmantar da al’umma game da kyawawan ayyukan da shugabanni suka yi, ko kuma su yi ƙorafe-ƙorafe ko soke-soke a kan  abubuwan da shugabanni ko yan siyasa suke aikatawa waɗanda ba su dace ba. Haka kuma su jawo hankalin masu zaɓe su zaɓi mutane nagari da suka dace a lokacin jefa ƙuria. Hakan zai kawo gyara ga kurakuran da shugabanni suke tafkawa a lokacin da suke gudanar da mulkinsu. Haƙƙin kowane shugaba ne ya aiwatar da alƙawuran da ya yi wa alumma a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe. Alƙawuran sukan haɗa da: Samar da ingantaccen ilimi da ruwan sha da hanyoyin sufuri da kiwon lafiya da bunƙasa aikin gona da samar da  tsaro da zaman lafiya da kuma bunƙasa tattalin arziki. Rashin cika waɗannan alƙawura kan sa a sami yan adawa su riƙa soke-soke da ƙorafe-ƙorafe domin su tunatar da masu mulki ko yan siyasa game da alƙawurran da suka yi wa jamaa a lokacin yaƙin neman zaɓe domin su gyara. Wannan bincike zai mayarda hankali ne a kan matsayin adawa a siyasa da amfaninta da illolinta da kuma rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen kawo gyara da sauyi mai ma’ana ga yadda ake gudanar da mulkin siyasa don amfanin talakawa da ƙasa baki ɗaya. 

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.042

    author/Aliyu Rabi’u Ɗangulbi

    journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 42