Sassaƙa Sana’ar Sakke: Nazarin Wasu Kayan Aikin Sassaƙa a Ƙasar Hausa

  Tsakure

  Babban dalilin gudanar da wannan bincike shi ne ganin cewa masassaƙa a ƙasar Hausa na da muhimmaci wajen samar da muhimman abubuwan da suke taimakawa wajen inganta tattalin arzikin Hausawa musamman abin da ya shafi sana’o’insu na gargajya. Masassaƙa na aiwatar da sana’arsu ne ta yin amfani da wasu kayayyaki da ke taimaka masu yayin da suke gudanar da sana’ar. Bisa ga wannan ake ganin ya dace a fayyace waɗannan kayayyaki domin al’umma ta san su, ta fahinci yadda ake amfani da su a wajen aiwatar da sana’ar. Wannan buƙatar ta taso ne ganin cewar da yawa daga cikin al’ummar ba su san su ba, balle su san yadda ake amfani da su. Manufar wannan bicike ita ce ƙoƙarin fito da nau’ukan kayan aikin sassaƙa da masassaƙa ke amfani da su a ƙasar Hausa. An aza wannan binciken bisa Ra’in Ayyukan Al’adu (Functional Theory of Culture) wanda aka ƙirƙiro tun a shekarun 1939 a ƙasar Czech. Masu rajin wannan ra’in suna ganin ana iya nazarin al’adun ne duba daga irin gudummawarsu wajen gina al’umma. Sun bayyana cewa, ɗaiɗaikun al’adu a cikin al’umma su ne musabbabin ginuwar a’umma. Dabarun binciken da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanai domin gudanar da wannan bincike sun kasu gida biyu, manya da ƙanana. Manyan hanyoyin sun haɗa da ziyarar gani da ido da tattaunawa da masana. Sauran ƙananan hanyoyin kuwa sun haɗa da binciken wasu ayyuka da aka buga da waɗanda ba a buga ba masu dangantaka da wannan bincike. A ƙarshe binciken ya gano nau’ukan kayayyaki daban-daban da yadda masassaƙa ke amfani da su wajen aiwatar da sana’ar sassaƙa a ƙasar Hausa.

  Fitilun Kalmomi: Sakke, Sassaƙa, Sana’a

   DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.030

  author/Rambo, A.R. & Aminu, N.

  journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 30