Tsakure
Zaurance yana ɗaya daga cikin azancin da harshen Hausa ya yi fice da su
wanda matasa musamman mata suke amfani da shi wajen sakaya zance ta hanyar
sauya masa wasu fitattun kamannin da aka san shi da su a harshe. Hikima
ce daɗaɗɗiya a adabin al’ummar Hausawa wadda matasa suke amfani
da ita a harshen Hausa domin isar da saƙwanninsu ba tare da wata matsala ba. Azanci da hikimar
zaurance suna da alaƙa da ilimin tasarifi da
kuma ilimin tsarin sautin Hausa. Wannan takarda ta yi ƙoƙarin bibiyar zaurance
a al’adar Hausawa da kuma alaƙarsa da ilimin tsarin sautin Hausa. Takardar ta
bayyana cewa lallai zaurance
wata hikima ce ta harshe wadda harshen Hausa ya yi fice da ita. Kasacewar zaurance
ya shafi adabin baka na Hausa kai tsaye, amma takardar ta fito da wasu muhimman
lamuran tsarin sauti, kamar saɓa ƙa’idar tabbatattun gaɓoɓin
kalmomin Hausa ta hanyar wasu ‘yan ƙare-ƙare da ake yi a kan gaɓoɓin a
yayin samar da shi. Haka kuma, akwai alamar ƙara saurin magana,
wadda takan taimaka wajen cikarsa.
Muhimman kalmomi: Zaurance, Tsarin Sauti, Azanci, Harshen Hausa
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.036
author/Muhammad Sulaiman Abdullahi
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 36