Tsakure
Batun nazarin mutuwar harshe, reshe na Ilimin Walwalar
Harshe, yana da matuƙar muhimmanci da ban sha’awa. Duk da yake ko a fagen
nazarin kimiyar harshe, batu ne wanda ba ya da farin jini ga manazarta Ilimin
Walwalar Harshe.
Wannan ya sa bai samu kulawar da ta kamace shi ba, musamman ma wajen manazarta harshen Hausa. Wannan ya sa aka ƙudurci kawo batun a bisa faifan nazari a wannan takarda. Yawancin bayanai da aka yi
a wannan nazarin an gina su ne a kan tafarkin bayanin mutuwar harshe na
Crystal (2003,
2014). Babban abin da
wannan takarda ta mayar wa hankali shi ne, fitowa da nazarin mutuwar harshe a
zahiri
a riƙa jin ɗuriyarsa a nazarin Hausa. Sakamakon nazari na
wannan takarda shi ne fitowa da ma’anar mutuwar harshe da nau’o’insa da
matakansa da mizanansa da ra’in nazarinsa da kuma keɓaɓɓun kalmomin nazarin mutuwar
harshe. Nazarin
yana da manyan sassa huɗu, su ne: Gabatarwa da
bayani a kan harshe da mutuwar harshe a ilimin kimiyyar harshe, sai sakamakon nazari da
kammalawa.