Tsakure
Nazarin ayyukan adabin Hausa a bisa wasu ayyanannun ra’o’i
abu ne da bai daɗe
da bayyana a duniyar nazari
ba. Da yawa
daga cikin marubuta adabin Hausa sukan yi rubuce-rubucensu ba tare da sanin
cewa aikinsu ya yi daidai da wani ra’i ba. Wasu masana suna ganin cewa,
wasu nau’ukan ra’in kamar ba su da muhalli a nazarin ayyukan adabin Hausa.
Wannan ne ya sa aka yi ƙoƙarin
ɗora ra’in Mararanci (Romanticism theory) da
manufofinsa
a rubutaccen
wasan kwaikwayon Hausa domin
ganin ko ana iya nazarin ayyukan adabin Hausa ta hanyar amfani da wani
ayyanannen ra’i . A wannan aiki an duba manufofin ra’in ne da yadda suke
wanzuwa a cikin ayyukan adabi, musamman wasan kwaikwayon Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen tattara bayanan da
aka yi amfani da su wajen wannan aiki, waɗanda suka haɗa da karance-karance a littafai domin samun ƙarin haske kan ra’in da aka ɗora
aikin, da kuma zaɓo wasan kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi wanda a kansa ne nazarin ya ta’allaƙa. Binciken
ya tabbatar da yiwuwar nazarin wasannin
kwaikwayon Hausa ta hanyar amfani da ra’in Mararanci. A ƙarshe
binciken ya gano cewa,
irin waɗannan wasannin kwaikwayon Hausa suna da matuƙar
tasiri a kan
abubuwan da suka shafi zamantakewar
al’umma.
Fitilun Kalmomi: Ra’i ,
Mararanci, Nazari, Wasan
Kwaikwayo
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.032
author/Jibril Yusuf
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 32