Tsakure
Shirya fim
babban aiki ne wanda duk mutumin da yake da sha’awar
ɗaukar nauyinsa yake fuskanta.
Bayanai a kan yadda shirya fim, yana buƙatar bin wasu matakai da tsare-tsare kafin a kai ga tabbatar
gundarin shirin cikin faifai zuwa ga masu kallo. Gabatar da shirya fim yana buƙatar ayyukan ƙwararrun mutane, masu
hikima da basira, kuma waɗanda
za su sa ido don ganin an gudanar da aikin da aka sa a gaba. Samar da ingantaccen
labari wanda za a iya gabatar da shi a matsayin fim, shi ne mataki na farko. Marubucin
labari kan yi tunanin irin abubuwa da ke faruwa a cikin al’umma, waɗanda ake son
a nuna domin su faɗakar da al’umma; tare da yin hannunka-mai-sanda zuwa
gare su. Dalili na neman samun ingantacciyar al’umma ne yake haifar da tunanin tsara
labari wanda zai faɗakar ko ya wa’azantar
ko kuma ya ilmantar. An gudanar da wannan nazari ne bisa manufar fito da hanyoyin
da masu shirya finafinan Hausa suke bi wajen lura da ƙa’idojin shirin
fim. Kazalika, an yi amfani da wasu hanyoyi domin samun bayanai. An duba wasu ayyuka
da suka gabata tare da tattaunawa da wasu nmasu ruwa-da-tsaki a harkar shirin finafinai. An leƙa zaurukan sada
zumunci domin samo wasu bayanai kamar ; Google da Youtube da Wikipedia da Facebook
da Opera da Acaemia. An ɗora wannan aikin
nazari a kan Nazarin Ƙwaƙwaf da Ƙwaƙƙwafi, masu ɗauke da ma’anar
‘Content Analysis’ da ‘Close Reading’, haka kuma nazarin ya gano cewa, a harkar
shirin finafinan Hausa, mafi yawanci ba su da takamaiman tsari na gudanarwa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.035
author/Dr Ibrahim Mohammed Gandu
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 35