Tsakure
Wannan aiki ne da ya yi
nazarin yadda aka yi amfani da harshe wajen fito da wasu ɗabi’un al’ummar da ke
rayuwa a cikin fada. Duk da cewa waɗannan ɗabi’u ana iya samun su a kusan kowane irin rukunin al’umma, to amma
kasancewar makaɗa Ibrahim Narambaɗa shahararren makaɗin fada wanda ya kwashe lokaci mai tsawo na rayuwarsa yana gogayya a fada
har ya kasance yakan rattabo wasu halaye da suka yi fice a fada ya-Allah a
wajen yin yabo ko zambo ko habaici da sauransu. Wannan maƙala ta nazarci wasu ɗiyan waƙoƙinsa da kuma fito tare da taskace waɗannan ɗabi’u da suka mamaye rayuwar fada. Wajen ganin an cimma wannan ƙudiri, binciken ya bi hanyar sauraron waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa da aka naɗa a faifan c.d tare da tattaunawa da wasu tsofaffin fadawa na fadar Zazzau
waɗanda suka yi mu’amala da Narambaɗa lokacin rayuwarsa. Binciken ya ƙara tabbatar da cewa, ana iya nazarin ɗabi’ar al’umma ta hanyar nazarin furucinsu.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.031
author/Muhammad, A.L. & Kyambo, S.B.
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 31