Tsakure
Rarrabe
tsakanin al’adun aure da Hausawa suka gada kaka da kakanni da abubuwan da
addinin Musulunci ya ya zo da su, ba abu ne mai sauƙi ba. Idan aka lura da irin tasirin da addinin Musulunci
ya yi a kusan dukkan É“angarorin rayuwa, za a ga cewa wasu abubuwa da suka shafi
aure sun sauya daga abin da al’ada ta zo da shi ya zuwa ga abin da addinin
Musulunci ya zo da shi. Musulunci ya zo da dukkan tsare-tsare, kuma rashin bin
wannan tsari na Musulunci, kan iya zama barazana ga auren ma’aurata da kuma
rayuwarsu ta gaba É—aya. Wannan
takarda na da manufar: bayyana auren Hausawa, ta kuma fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa tare da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa. Hanyar da aka bi
wajen aiwatar da wannan bincike ta haÉ—a da hira da wasu mutane da karance-karancen littattafai da kundayen
binjcike. An É—ora wannan maÆ™alar a kan ra’in Sauyin al’adu. MaÆ™alar, ta fito da irin tasirin da Musulunci ya yi a
wasu al’adun Hausawa na aure, tun daga kore wasu, sauya wasu, da kuma samar da
wasu al’adun.
Keywords: Al’ada, aure, Musulunci da tasiri
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.026
author/Maikwari, H.U. & Lawan, M.S.
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 26