Tsakure:
Awon baka wani reshe ne na nazarin waƙoƙin baka. Wannan fagen nazari ya shafi yadda makaɗi yake shirya waƙa a cikin zubin ɗiya da dabarun karin murya. A ɓangaren ana duba zubin layuka da yawan ɗiyan waƙa da tsarin rerawa da karin murya da amsa-amon kari da sauran abubuwan da suka shafi awon baka. (Gusau, 2003, sh. 32). Don haka, wannan aiki kacokan ɗinsa an ɗora shi ne a kan ra’in waƙar baka Bahaushiya, wanda Gusau (2003) ya samar. Takardar ta duba karin murya ne a waƙar Sarkin Kudu Macciɗo ta Makaɗa Sa’idu Faru. Kamar yadda aka sani, karin murya ya ƙunshi amsa-amon kari da gidan dara na kari, waɗanda suke wani ɓangare ne na awon baka. A taƙaice dai, a takardar an kawo Taƙaitaccen tarihin makaɗa Sa’idu faru da ma’anar waƙar baka da ma’anar awon baka da ma’anar karin murya da ma’anar amsa-amon kari da kuma ma’anar gidan dara na kari. Sannan aka nazarci amsa-amon kari da gidan dara na kari a waƙar. An yi amfani da dabarar sauraro da karance-karancen littattafai da mujallu da muƙalu da kuma kundayen bincike wajen tattaro bayanan gudanar da wannan takarda. Daga ƙarshe ana fatan wannan bincike zai fito da bayanin yadda makaɗin yake sarrafa muryarsa wajen ƙulla waƙoƙinsa.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Awon Baka, Kari, Rauji
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.052
author/Jamilu Alhassan & Halima Mansur Kurawa
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 52