Tsakure:
Wannan muƙala tana ƙoƙarin fito da wasu kalmomi na musamman waɗanda marigayi makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a wasu daga cikin waƙoƙinsa, a inda yake ambaton kalma tare da kawo akasinta ta hanyar nuna fifiko ko kasawa a tsakanin Sarakuna da mabiyansu ko abokan hamayyarsu. Irin waɗannan kalmomi sukan zo a cikin salon Mutuntarwa ko Dabbantarwa ko kuma Abuntarwa. Hakan yana faruwa ne a lokacin da yake yin zuga ko kwarzanta gwanayensa Sarakuna a cikin wasu ɗiyoyin waƙoƙinsa. Haka kuma, su irin waɗannan kalmomi suna iya zama sunaye ko wasu siffofi. A nan, an yi amfani da Ra’in dangantakar Tunani da Ma’ana (Mental Theory of Meaning) wanda John Locke (1689) ya ɓullo da shi, sannan Bertrand Russell (1970) da Neil Skinner (1971) suka yi amfani da shi a cikin ayyukansu. Wannan ra’i yana magana ne a kan ma’anonin kalmomi masu kishi da juna wajen bambanci da kuma yin zuzzurfan tunani kafin a gano bambancin nasu ta fuskar harshe ko al’ada. Domin kuwa, ra’in yana nuna yadda akan yi amfani da kalmomi wajen yin nazari da tunani ko samun manufofi a rayuwa. Sannan an gudanar da binciken ne ta hanyar saurare tare da yin nazari da kuma juyar sautin waƙa watau ‘Transcription’. Maƙalar ta gano cewa, yin amfani da irin waɗannan kalmomi yana bai wa mai sauraro shauƙi wajen sauraro tare da fahintar harshe ko samun ƙwarewa da gwanintar harshe daga bakin makaɗa. Domin kuwa, hakan ya taimaka sosai wajen bunƙasa harshen Hausa da al’adun Hausawa. Misali; a cikin waƙarsa ta Marigayi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai taken ‘Kana shire Babban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo’ inda ya ambaci kalmomin kyawo da mummuna, samu da busasshe, mutum mai iko da mai roƙonsa da sauransu. Saboda haka, ɗalibai da sauran masu nazari za su iya fahinta tare da nazarin rukunin kalmomi da ma’anoninsu ta hanyar sauraron irin waɗannan waƙoƙi na baka masu muhimmanci a harshe.
Fitilun Kalmomi: Waƙa, Kishiyar Ma’ana, Fifiko da Kasawa
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.053
author/Abdullahi Bashir & Abu-Yazid Ishaq Yusuf
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 53