Tsakure:
Ma’aunin Waƙa ra’i ne da ake amfani da shi wajen auna waƙoƙin Hausa, musamman na baka. Manufar wannan takarda ita ce auna wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru a kan Bahaushen kari na cikin Ma’aunin waƙa, domin a gano dacewarsu a kan karuruwan. An yi amfani da littattafai da kundaye da mujallu da muƙalu a matsayin hanyoyin tattaro bayanai na gudanar da wannan bincike. A ƙarshe an auna waƙoƙi guda bakwai, kuma kowacce ta hau karin da ya dace da ita, daga cikin karuruwan da aka tanadar na Bahaushen kari, da suka haɗa da: Cikakken kari da kari mai dungu ɗaya da kari mai dungu biyu da Kari mai wushirya da kari mai cassawai da kari mai giɓi gaba da kuma kari mai giɓi baya. Ana sa ran wannan bincike zai zama zakaran gwajin dafi wajen ɗaukar waƙoƙin baka a auna su, domin sanin tsayayyen karin da makaɗin ya yi amfani da shi domin ƙulla waƙar tasa.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Ma’auni da Cassawai da
Wushirya da Kari da Illa da kuma sauyi
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.051
author/Hauwa Abubakar Isma’il & Jamilu Alhassan
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 51