Dabbobi Da Ƙwari Da Tsuntsaye a Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Waƙa babban tafarki ce na bayyana falsafar mawaƙa wajen ilmantarwa a fannin adabi da sauran fannonin ilimi. Ana kuma iya kallom saƙonnin da ke ƙunshe a cikin waƙoƙi ta fuskoki da dama. Wannan bincike ya yi bayani ne a kan dabbobi da ƙwari da kuma tsuntsayen da makaɗa Sa’idu Faru ya ambata a cikin waƙoƙinsa, inda ya yi amfani ne da su domin ya fito da wasu halaye na waɗanda yake yi wa waƙa, ta hanyar nuna zaruntaka ko ƙwazo ko kasawa ko yaba masu ta ɓangarori daban-daban na rayuwa, ko amanarsu ko adalcinsu da sauransu. Manufar wannan bincike ita ce fito da dabbobi da tsuntsaye da kuma ƙwarin da makaɗa Sa’idu faru ya ambata a cikin waƙoƙinsa. Sai kuma fito da muhimancin dabbobi da ƙwari da tsuntsaye ga Bahaushe wajen gina adabinsa, don faɗaɗa ilimi da kuma raya adabin Hausa. Binciken ya gano cewa lura ita ce mizanin gano duk wata ɗabi’a ko wani hali na duk wata halitta. Da shi ne mawaƙan suka yi amfani suka gano halaye da ɗabi’un dabbbobi da ƙwari da tsuntsaye har suka fara bayyana su a cikin waƙoƙin.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.020

    author/Dr. Sani Yahaya Mafara & Dano Balarabe Bunza, (Ph.D)

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 20