Nazarin Turken Yabo Da Zuga A Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Babban maƙasudin wannan takarda shi ne Nazarin turken yabo da zuga a wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Amfanin da turken yabo da zuga a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani saƙo ne na nuna yabo da kuma zuga ga wanda ya yi wata kyauta da kuma nuna bajinta ko ƙwazo. Makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin irin mawaƙan da suka yin amfani da irin waɗannan turaku don haka ne wannan muƙala ta yi nazarin yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da waɗannan turaku a cikin waƙoƙinsa. A wajen gudanar da wannan bincike an bi hanyoyin samun bayanai da suka haɗa da tattara waƙoƙin Alhaji Saidu Faru musamman waɗanda suka shafi wannan nazari sannan kuma an nazarci bugaggun littattafai da kundayen bincike da takardu na ilimi. Bayan haka an tattauna da masana da manazartaadabin da harshe domin samun ingantattun bayanai. A ƙoƙarin cimma manufa, an yi amfani da mazhabar waƙar Baka Bahaushiya wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar Baka Bahaushiya. Wanda ya jagoranci wannan mazhabar shi ne Saidu Muhammad Gusau. Bayan kammala wannan muƙala an lura da cewa makaɗa Sa’idu Faru yana amfani da turken yabo da zuga a cikin waƙoƙinsa.

    Fitilun Kalmomi: Yabo, Zuga, Gwarzantawa, Caccaɓawa, Kururutawa

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.018

    author/Malumfashi, A.S., Galadima, S.S. & Jangebe, S.A.

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 18