Dangantakar Adabi Da Tarihi: Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar a Bakin Sa’idu Faru (Malamin Waƙa, Maikwana Ɗumi Na Mamman Na Balaraba)

    Tsakure: 

    Adabin baka na Hausa wani babban kogi ne da sai dai a kamfata a bar shi, a ƙarƙashinsa aka samar da gurbin makaɗan fada, makaɗan da ke yi wa sarakuna kiɗa da waƙoƙin yabo da zuga da kwarzanta su, sukan kuma bayyana wasu kyawawan halayensu da nasabar iyayen gidansu. Makaɗa Sa’idu Faru (Malamin waƙa) ya kasance makaɗin Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar lokacin yana Sarkin Kudu, watau uban ƙasar Talatar Mafara. Waƙoƙin da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo cike suke da ambaton nasaba da yabo da tarihi da fata da sauransu, masu iya magana na cewa: “Kyawon maroƙi ya roƙe ka da iyayenka.” Manufar wannan takarda ita ce fakewa da wasu waƙoƙin da malamin waƙa Sa’idu Faru ya yi da ya bayyana asali da nasaba da kuma halayen Sarkin Kudun Sakkwato. Domin tabbatar da wannan batu, an saurari fayafayai da mawaƙin ya yi lokacin rayuwarsa, an duba litattafai da masana suka rubuta da ke da alaƙa da wannan batu. Har wa yau, an kuma duba muƙalu. Nazarin ya gano cewa Sa’idu Faru (Malamin waƙa) ya naƙalci harshen da yake waƙa da shi, wannan ya ba shi damar zaɓen kalmomin da yake ƙulla zaren waƙoƙinsa su dace da turakun da ya ɗora waƙarsa a kai.

    Keɓaɓɓun Kalmomi: Adabin baka da tarihi da waƙa da Sa’idu Faru da Sarkin Musulmi Macciɗo

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.040

    author/Abubakar Ɗalha Bakori, Sulaiman Adamu & Yusuf Ibrahim Zuntu

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 40