Tsakure:
A
wannan takarda, an nazarci yabo a cikin wasu waƙoƙin
makaɗa
Sa’idu Faru. An zaɓi wasu daga cikin waƙoƙinsa aka fito da ɗiyan waƙoƙin
da suke ƙunshe da yabo ta fuskar addini, da yabo
ta fuskar asali, da yabo ta fuskar jarunta da kuma yabo ta fuskar kyauta,
sannan aka yi sharhi gwargwadon fahimta. An ɗora wannan aiki a bisa ra’in mazhabar
Waƙar Baka Bahaushiya wadda Gusau (2003 da
2015) ya assasa. An tattaro wasu matanonin waƙoƙin
Sa’idu Faru ta hanyar amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Gusau (2009), da kuma
sauraron wasu waƙoƙin tare da rubuta matanoninsu a
takarda. Binciken ya gano cewa Sa’idu Faru
ya ƙware wajen yabon sarakuna da ‘ya’yan
sarakuna ta hanyar kawo sunayen iyayensu da kakanninsu da danganta su da su,
tare da nuna cewa suna da asali mai kyau, kuma sun gaji kula da addini da
jarunta daga wajen iyaye da kakanni. Haka kuma Sa’idu Faru mawaƙi
ne wanda yake bayyana kyautar da aka yi masa, saboda haka ne waƙoƙinsa
suke ƙunshe da yabon waɗanda suka yi masa kyauta ko wata
hidima. A taƙaice, an fahimci cewa ɗiyan waƙoƙin
da suke ɗauke da yabo a waƙoƙin Sa’idu Faru suna ƙara
ɗaukaka darajar waɗanda yake yabon, kuma suna ilmantar da
al’umma tarihin wasu masarautu da kuma wasu muhimman mutane. Haka kuma ɗiyan waƙoƙin
da suke ɗauke da yabon, suna ilmantar da al’umma muhimmancin kula da
addini da kyauta da kuma jarunta.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.039
author/Aminu Ibrahim Bunguɗu, Hassan Isa & Aliyu Rabi’u Ɗangulbi
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 39