Mabuɗin Tarihin Rayuwa Da Fasahohi Da Matakan Shiryawa Da Aiwatar Da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru (1932-1987)

    Gabatarwa

    Tun ran gini ran zane, tun da Hausawa suka zauni Ƙasar Hausa suke shiryawa da aiwatar da waƙoƙin Baka na Hausa. Haƙiƙa, Hausawa sun jima ainun suna rera waƙoƙin baka da ka har kuwa zuwa lokacin da suka ƙirƙiri wasu sinadarai na gwama waƙar baka da kiɗa. Kamar yadda ake nunawa, a Ƙasar Hausar Hausa[1] an fara waƙoƙi ne na dandali da na soyayya[2]. Da Hausawa suka sami fasaha ta kayan kiɗa, sai suka durmuya cikin waƙoƙi na farauta da na tauri da na siddabaru ko wobuwa ko waɗanda suke da wata ɗaukaka a rayuwa ta mutane da makamantan waɗannan. Daga nan ne makaɗa suka saki jiki suka dinga yi wa Sarakuna da sauran masu jini na Sarauta Waƙoƙi (Gusau, S. M. (1983).

    author/Sa’idu Muhammad Gusau

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 04