Tsakure:
Makaɗa
Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin
shahararrun makaɗan fada na ƙasar
Hausa. Yawancin waƙoƙin
makaɗan fada na ƙasar
Hausa sun fi karkata kan turken zambo, yabo, zuga, koɗa
kai, ban-dariya da addini, musamman ga maza. Sannan kuma, makaɗan
ba su cika yi wa mata waƙa
ba, ballantana su faɗi
wata daraja da baiwa da Allah Ya yi wa mata. Ta haka ne wannan takarda ta duba
yadda Sa’idu Faru ya nuna muhimmancin mata da irin gudunmawar suke bayarwa a
cikin waƙar “Mai Babban Ɗakin
Ƙasar
Kano.”
Wannan waƙa ta taimaka wajen
nuna cewa su ma makaɗan
fada ba a bar su a baya ba wajen nuna matsayin mata a cikin al’umma. Manufar
takardar, ta yi nazarin wannan waƙa ta
fito da irin muhimmancin da makaɗin
ya ba mata. Hanyoyin tara bayanai sun haɗa
da: wallafe-wallafe da faifai na CD da aka yi a kan waƙoƙinsa.
Wannan bincike zai taimaka wajen fahimtar irin gudunmawar da mata suke bayar wa
a cikin al’umma, musamman don jin haka daga bakin makaɗi
irin Sa’idu Faru. Haka kuma, binciken zai kuma buɗe ƙofar
nazarin fannonin adabi daban-daban.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.027
author/Zainab Isah
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 27