Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari a Waƙar Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda

    Tsakure: 

    Wannan bincike ya yi nazarin salon sarrafa harshe a ɗaya daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Nazarin wanda ya karkata a nazarin salon sarrafa harshe a fannin kimiyyar harshe, ya duba salon zaɓen kalmomi na Sa’idu Faru a waƙarsa ta Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda. An yi amfani da hanyar nazarin salo da sarrafa harshe na Leech da Short (1981) aka aiwatar da nazarin. Waƙar wadda ita ce babbar ginshiƙi a bayanai da binciken yake buƙata an same ta ne a kafar sadarwa da kuma rubutacciyar ta a diwani da manazarta suka tattara na wasu waƙoƙin baka. Binciken ya nuna irin kalmomin rukunan nahawu da aka yi amfani da su musamman Suna, da Wakilin suna, da Aikatau, da Bayanau. An kuma yi nazarin nau’o’in Adon Magana a waƙar da makaɗin ya yi amfani da su, musamman Siffantawa da Jinsintarwa. Haka nan an ga irin ganguna da makaɗin ya faye amfani da su da yadda duka waɗannan sassa manya da ƙanana na nahawu da adon magana suka taimaka wajen isar da manya da ƙananan saƙonnin cikin waƙar.

    Keɓaɓɓun Kalmomin Nazari: Salo, Sarrafa Harshe, Nazari, Suna, Aikatau

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.026

    author/Ibrahim Lamido PhD & Bara’atu Inuwa Maikadara

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 26