Tsakure:
Ayyukan da aka yi kan adabin waƙa sun fi na kowane ɓangaren adabi yawa a nazarin Hausa. Mawaƙan baka na Hausa ba lungun rayuwar Hausawa da ba su waƙe ba. Sa’idu Faru a cikin makaɗan fada ba ƙyalle ne ba. Alhaji Muhammadu Macciɗo Sarkin Kudun Sakkwato ne maigidansa. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Sarkauna da ‘ya’yan sarauta da yawa waƙa, amma na Sarkin Kudu Macciɗo sun fi yawa da shahara. An yi amfani da dabarar bincike ta ga-wuta-ga-masara wajen tace waƙoƙinsa domin a hango wuraren da ya yi kukan kurciya game da yadda maigidansa zai kasance. A taƙaice, duk wanka da kamar jurwayen da ya yi na fatar Sarkin Kudu Macciɗo ya kasance jagoran gidansu da hawa gadon sarautar Sarkin Musulmi sun tabbata bisa ga kasancewarsa Sarkin Musulmi na (19). Tunaninsa na yadda zaɓen Sarkin Musulmi Macciɗo zai kasance ya tabbata. Yadda ya yi hasashen mutuwarsa haka ya kasance. Da yawa jifa cikin duhu yana kasancewa kamar ga bakin boka, haka ko ta kasance. Akwai buƙatar manazarta adabi su fara tunanin nazarin adabinsu a kimiyance fiye da tsayawa kan salo da jigo da turakun tussan adabinsu. Sakamakon wannan ɗan nazari ya nuna muna ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Samun sababbin abubuwa cikin adabin yanzu aka fara. Kowane zango na adabi da ire-iren abubuwan da za a tsinta a ciki.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.003
author/Aliyu Muhammadu Bunza
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 03