Tsakure:
Wannan muƙala ta mayar da hankali ne wajen gano wuraren da makaɗa Sa’idu Faru ya yi
amfani da turken koɗa kai a cikin wasu waƙoƙinsa. Manufar binciken ita ce fito da hikimomin Uban kiɗi na amfani da wannan
turken a wasu waƙoƙinsa waɗanda ya riƙa yi wa jama’a daban-daban. Ra’in da aka yi amfani da shi a wannan aikin
binciken shi ne ra’in Waƙar Baka Bahaushiya na
Gusau (2003). Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanan wannan
aikin sun haɗa da sauraren waƙoƙin Malamin waƙa wato makaɗa Sa’idu Faru tare da tattaunawa da wasu masana da masu sha’awar nazarin
waƙoƙin nasa. Akwai wasu waƙoƙin da ya yi amfani da
wannan tubalin ginin turken kamar yadda wannan binciken ya gano domin ba dukan
waƙoƙin nasa ne ya yi hakan
ba, sai dai a kalli waƙoƙin a zaƙulo irin wannan turken
na koɗa kai.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.037
author/Dr. Haruna U. Bunguɗu, Muhammad S. Abubakar & Muhammad A. Saleh
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 37