Tsakure:
Salon magana maganganu ne na hikima da kakkarya harshe waɗanda ake yi ta hanyar sarƙa kalmomi masu sauti iri ɗaya a cikin jimla ko jimloli, a yi magana mai sarƙaƙiya. Irin wannan
shi wasu ke kira Ƙarangiya ko gagara-gwari. Manufar wannan maƙala ita ce fito da wasu ɗiyan
waƙoƙi da ke ɗauke da salon magana, tare da yin sharhi gwargwadon fahimta. Maƙalar za ta mayar da hankali ne ga wasu salailan maganganu guda biyu da Sa’idu
Faru ya yi amfani da
su a cikin waƙar
Sarkin Yaƙin
Banga. An ɗora wannan aiki a bisa ra’in Mazhabar
Waƙar
Baka Bahaushiya wadda Gusau (2003) ya assasa. An samu wannan waƙa faifan CD, sannan aka saurare ta,
tare da rubuta matanonin ta a kan takarda. An tattauna da wasu masana da
manazarta domin ƙara
samun haske. Haka kuma an duba wasu littattafai da kundayen bincike da maƙalu domin ƙara samun wasu muhimman bayanai. An
gano cewa makaɗa Sa’idu Faru mutum ne mai basira wanda
ya ƙware
wajen sarrafa harshen Hausa. Saboda haka ne ake samun salon magana a cikin wasu
ɗiyan waƙoƙinsa. Haka kuma, an gano cewa, kalmomin gagara-gwari ko ƙarangiya suna da
mutuƙar wahalar ambato ga waɗanda ba Hausawa ba har da ma Hausawan. Musamman idan ana magana ko maimaita
waɗannan maganganu da
sauri-sauri.
Muhimman Kalmomi: Gagara-Gwari, Ƙarangiya, Makala, Ra’i, Waƙar Baka da kuma Salon
Magana
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.036
author/Samaila Yahaya & Bello Almu
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 36