Tsakure:
Sa’idu
Faru, makaɗi ne
wanda yake shirya waƙoƙinsa a
kan manufofi daban-daban kuma manya da ƙanana. Haka kuma yakan lura da yanayin mutane da kuma sauran abubuwan da suke
kewaye da su, musamman ta yanayin halaye da ɗab’iunsu. Hakan ta sa yake amfani da wannan dama
ya ambaci wasu dabbobi a zubin ɗiyan waƙoƙinsa domin fito da danganta ta halaye ko kuma
danganta wani da hali ko halaye da wata dabba don habaici ko don yin hannunka-mai-sanda. Haka kuma, yakan fito da wasu halayen
dabbobin ta hanyar jingina su ga mutane, musamman ta la’akari da mu’amalarsu ta
yau da kullum. A wannan takarda an yi amfani da hanyar nazarin waƙar baka Bahaushiya ta Gusau (2014). Haka kuma, hanyoyin tattara bayanai
an yi amfani da Mp3 na wasu waƙoƙin da kuma samo wasu ɗiyan waƙoƙi a Diwanin waƙoƙin baka na Hausa na Gusau (2009). Har ila yau,
an fahimci Sa’idu Faru yana lura da
halaye da ɗabi’u na dabbobi a wajen tsarma su a
matsayin tubali a wasu waƙoƙinsa. Haka kuma an lura Sa’idu Faru yana
amfani da halaye da ɗabi’un wasu dabbobi ya alaƙanta su da wasu mutane a cikin al’umma. Ta hanyar lura da
yanayin rayuwar dabbobi da kuma fito da ita a cikin zubin ɗiyan wasu waƙoƙinsu su tare da danganta mutane da ita domin
yaba musu ko kushe musu,saboda wasu dabbobin suna da yanayin halaye da mutane
sukan aikata yau da kullum a zamantakewarsu. Misali kamar; kwaɗayi ko faɗa ko ɓarna ko haƙuri ko dabara ko haɗari ko ƙarfi ko munafinci da sauransu.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.038
author/Dr. Umma Aminu Inuwa
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 38