Tsakure:
Wannan muƙala ta mayar da hankali ne wajen gano ire-iren dabbobi da tsuntsaye da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a zubin waƙoƙinsa. Manufar binciken ita ce fito da hikimomin Uban kiɗi na amfani da dabbobi da tsuntsaye wajen fitar da ma’anoni a wasu waƙoƙinsa waɗanda ya riƙa yi wa jama’a daban-daban. Ra’in da aka yi amfani da shi a wannan aikin binciken shi ne ra’in waƙar baka Bahaushiya na Gusau (2003). Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanan wannan aikin sun haɗa da sauraren waƙoƙin Malamin waƙa wato makaɗa Sa’idu Faru tare da tattaunawa da wasu masana da masu sha’awar nazarin waƙoƙin nasa. Bugu da ƙari, ba a iyakance yawan waƙoƙin da za a nemo sunayen waɗannan dabbobi da tsuntsaye da makaɗin ya yi amfani da su ba, domin ba dukan waƙoƙin nasa ne ya yi hakan ba, sai dai a kalli waƙoƙin a zaƙulo ire-iren waɗannan turakun.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.035
author/Dr. Haruna Umar Bunguɗu & Hauwa Tanko Idris
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 35