Tsakure:
Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. Wannan muƙalar tana ɗauke da bayanin yadda wasu al’adun Hausa suka yi rabuwar dutsi-hannun-riga da na ƙabilar Barebari dangane da yanayin zamantakewa a cikin al’umma. Manufar wannan takardar shi ne bayyana wasu al’adun Hausawa a sarari da kuma na Barebari. Haka kuma, takardar ta yi amfani da hanyoyi guda biyu domin tattara bayanai da nufin cimma ƙudurinta wajen samun ingantattun bayanai. A nan, an yi hirarraki da tambayoyi da sauraro a fakaice. Sannan ɗaya hanyar ita ce, karance-karancen littattafai da kundayen bincike da muƙalun da aka gabatar a tarukan ƙara wa juna ilimi da ma bugaaggun muƙalun. Muƙalar tana ɗauke da zaɓi na kan mai uwa da wabi (Random Sampling). Bayan haka, sakamakon binciken ya bayyana bambancin wasu al’adun Hausawa da na Barebari ta fuskar al’adun gaisuwa da na sutura(tufafi) da na abinci da al’adar saukar baƙo. Daga ƙarshe, muna sa ran takardar ta zamo alfanu ga al’ummar Hausawa da manazarta al’ada da ma sauran masu masu nazari.
Muhimman Batutuwa: Al’adar Gaisuwa da Sutura da Abinci da Karɓar Baƙo da kuma YanayiDOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.022
author/Babangida, A., Abubakar, I. & Muhammad, N.A.
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |