Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada

    Tsakure: 

    Munafar wannan takarda ita ce fito da amfanin izga a tunanin Hausawa a wajen amfani na yau da kullum da kuma wajen magance wasu cututtuka, musamman a mahangar ‘yanbori. Haka kuma, an yi amfani da hanyar tattaunawa wajen tattaro bayanan wannan bincike da kuma hanyar ziyartar masu aiwatar da bori. Haka kuma, a wannan bincike an lura ‘yan bori da wanzamai sun fi amfani da izga wajen gudanar da ayyukansu, sannan kuma, wasu Hausawa suna amfani da izga wajen kaɗe ƙura musamman ‘yan kasuwa. Har ila yau, an gano yawanci ayyukan ‘yan bori a yau sun samu koma baya sakamakon zuwan addinin Musulunci. Har wa yau, an fahimci cewa izga tana taka muhimmiyar rawa wajen warkar da cutar iska. Hakazalika, a fahimtar wasu rukuni na al’ummar Hausawa suna yi wa waɗanda suke amfani da izga kallon sun kauce wa hanya, saboda tasirin addinin Musulunci. A yau, mutane sun fi amfani da hanyar ruƙiya wajen warkar da cutar aljanu maimakon zuwa wajen ‘yan bori. Masu bayar da magunguna a yau suna amfani da addu’o’i domin neman waraka, saɓanin a da, inda ake amfani da aljanu ko bokaye domin magance wata cuta da aka kasa gano kan ta. Ana amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen bayyana yadda ake warkar da marasa lafiya ta hanyar bori ko ruƙiyya a Fesbuk da Was’af da Tuwita da Tiktok da sauransu.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.023

    author/Maryam Mansur Yola

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |