Mace a Rubutaccen Habarce: Nazari Daga Littafin Jiki Magayi

    Tsakure: 

    Adabi rumbu ne wanda Bahaushe yake amfani da shi wajen warware duk wani abu da ya dame shi a rayuwarsa da ta ‘yan’uwansa. Bahaushe yana amfani da karin magana ko tatsuniya ko waƙa ko kuma tarihi wajen ilmantar da al’umma. Domin ya ɗauke su a matsayin makarantar farko da ake amfani da ita wajen ilmantarwa. Kodayake wannan muƙala an yi ƙoƙari wajen fito da ɗabi’un mace wanda marubutan littafin Jiki Magayi suka yi wato Tafida da East, domin a fito da darussa game da halin mata a cikin littafin. Kamar yadda bayanai suka gabata an nuna mace a matsayin tubalin gina al’umma wajen nuna halaye ko ɗabi’u da ya kamata su yi koyi da su waɗanda ya kamata su kiyaye, adabi yana taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al’umma ta fannin zamantakewa.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.021

    author/Ramatu Ishaq

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |