Basira Da Aiki Da Basira a Harshen Mata Hausawa

    Tsakure: 
    Takarda ce da aka yi yunƙuri domin ankarar da yadda ake amfani da basira a cikin zantukan mata Hausawa. Nazarin ya tabbatar da cewa mata na da basira da aiki da basira a cikin zantukansu na yau da kullum. Sakamakon Takardar ta gano tun tan gini tun rane, mata Hausawa na amfani da basira da aiki da basira tun fil azal, amma yau da gobe al’amuran zalaƙa da fasaha da hikima na ƙara bunƙasa kamar yadda binciken ya gano ya ba da misalai. Haka kuma mata na da rukunoni da dama waɗanda suke bayyanar da basirar amfani da harshe kamar yadda maƙalar ta gano. Manufar wannan maƙala ita ce ta fito da waɗannan bayanai a fili domin amfanin masana da manazarta harshen Hausa, musamman ta fuskar walwalar harshe. An yi amfani da ra’in siffantawa (Descriptive Theory) domin yi bayyanin wannan maƙala, kasancewar duk wani aiki da ya shafi nazarin walwalar harshe a kan sami nasarar bincike, in an ɗora shi a kan wannan ra’i. Haka kuma an yi amfani da littafai da maƙaloli da masana da manzarta suka rubuta wajen waiwayan aikin da suka gabata. Sannan an saurari maganganun mata Hausawa a matsayin masu ruwa da tsaki. A ƙarshe ana fatan wannan aiki ya zama mai amfani ga manazarta walwalan ilimin harshe.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.024

    author/Abdullahi Lawal Dikko (Ph.D)

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |