Tsakure:
Wannan maƙala mai taken: “Fasahar Bincike na Haƙiƙa: Jagoran Ɗalibai Cikin Aikin
Bincike.” Bincike na haƙiƙa shi ne irin nau’in binciken da ake yi na
ilimi. Wannan bincike dai shi ne gano wani abu da ya faku ko ya ɓoyu a wani sashen na
daban. Manufar wannan maƙala ita ce fito da aikin
bincike na haƙiƙa da matakan da za a bi wajen yin sa. Haka kuma wannan maƙala jagora ce ga ɗalibai masu aikin bincike. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙalar ita ce, ta karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen
bincike da mujallu na ilimi daga makarantu daban-daban. An kuma zaɓi a ɗora wannan binciken (Maƙala) a kan ra’in kwaɗaitarwa (Motivation Theory) wanda aka fi
danganta samuwarsa daga MC Dougal, (1871). Sakamakon binciken da
wannan maƙalar ta fitar shi ne, an
gano cewa bincike na haƙiƙa yana buƙatar bin wasu matakai da
suka danganci duban matsala, ziyarar muhallin da za a gudanar da wannan bincike
wato inda matsalar take, tattaunawa da wasu masu ilimi kan abin da ake bincike
a kai, samun kayan aiki, (data), yin amfani da fasahar zamani (SPSS) domin
nazartar kayan aikin (analysis), fitar da sakamakon abin da aka bincika.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.025
author/Haruna Umar Maikwari & Habibu Lawali Ƙaura
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |