Tsakure:
Wannan maƙala ce da ta shafi cuta da magani, domin game da sha’anin magani a kan wata cuta ko rashin lafiya, Bahaushe ya yi amanna da cewa “Ciwo ka Fidda Ciwo”. Akan sha ko shafa magani, ko shaƙensa domin magance cuta ko ciwo. Sai dai wannan maƙala ta fahimci cewa a gargajiyance akan yi amfani da wasu hanyoyin warkarwa masu zafi ko ciwo a matsayin magani ga mutane ko dabbobi. A nan, tunanin shi ne wace irin falsafa ko hikima ce ke tare da warkar da cuta ta amfani da zafi ko ciwo, kuma wane tasiri hakan ke da shi ga rashin lafiya ko maras lafiya. Manufar maƙalar ita ce duba ire-iren cututtukan da ake warkarwa ta amfani da wani nau’in magunguna masu ciwo ko raɗaɗi da zogi da yadda ake yin su, a kuma haƙiƙance dalilan da suka haifar da amfani da wannan hanya a matsayin magani. Haka za a yi ƙoƙarin gano matsayin al’adun gargajiya da tasirin zamani a wannan haujin magani. Za a yi amfani da salon bincike na bin diddigin cututtuka da magani da kwatance da tattaunawa da muhawara domin fitar da bayanai da za su iya tabbatar da amfanin matsalar da ake bincike ga al’ummar Hausawa ta amfani da ra’in Aiki da Fa’idantuwa na (Functional Theory). Maƙalar ta yi matsayar cewa “ciwo ka fidda ciwo”, sai dai akwai buƙatar juriya da ɗaukar matakai da za su inganta lafiya ga marasa lafiya da ake yi wa magani ta amfani da wata hanya mai zafi.
Muhimman Kalmomi: Ciwo da Gargajiya da Zamani da Magani da WarakaDOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.029
author/Dr. Nasiru Aminu
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |