Tsakure:
Tunanin aiwatar da wannan nazari ya taso ne ta la’akari da yadda ake samun tasirin zamantakewa a tsakanin Hausawa da makwaftansu na kusa da nesa, wanda abin bai tsaya a mu’amula ka]ai ba, har da dabarunsu na magani da warkarwa. A dalilin haka ne wannan bincike ƙuduri anniyar nazari a kan yadda baƙi na kusa da na nesa suka yi tasiri a kan magungunan Hausawa na gargajiya. Daga cikin irin yadda wannan bincike zai mai da hankali wajen bincikowa shi ne fito da yadda aka samu magungunan wasu baƙi na kusa da nesa suka yi tasiri a cikin al’ummar Hausawa da suke amfani da magungunansu ta fuskar kawar da cuta daga jikinsu, wanda su Hausawa mutane ne waɗanda suke da magungunansu na gargajiya tun iyaye da kakanni. Haka kuma, za a ɗora wannan bincike ne a kan Ra’i Ma yi ma gani (Therory of Trial and Error) Edward Lee Theradile ne ya ƙirƙiro shi a shekarar 1979. Sannan kuma,wajen gudanar da wannan bincike ana saran za a yi amfani da hanyar bincike ta tattaunawa da masana da masu aiwatar da sana’o’in magungunan Hausawa na grgajiya da kuma baƙi masu sana’ar sayar da magani na kusa da nesa, tare da nazari a kan abubuwan da suka shafi magungunan Hausawa na gargajiya. Daga ƙarshe ana saran wannan bincike zai binciko yadda al’ummar Huasawa suka rungumi magungunan baƙi na kusa da nesa suka saki nasu na gargajya a matsayin maganinsu na yau da gobe.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Cuta da magani da baƙi da Nupawa da Larabawa da TurawaDOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.030
author/Aminu Alhassan Idris & Nuhu Abbullahi Jibril
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |