Tsakure:
Babbar
manufar wannan takarda ita ce fito da matsayin mata a wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanƙwairo ta sigar yabo. Dalilin da ya sa
mutane ba su yi rubutu sosai ba, saboda hankali bai koma kai ba. Akwai wani
ilimi a ɓoye, wanda makaɗa suke bijiro da shi, wanda in an yi
nazarin sa za a samu ƙaruwa wajen rubutun yau da kullum. Don
rayuwar al’umma da sauran su a fagen nazari. An ɗora wannan binciken a kan ra’in Waƙar
Baka Bahaushiya (WBB) wadda Gusau (2015) ya assasa. Wanda yake Magana musamman
a kan sanin sunan makaɗi da tarihinsa da kuma ayyana tubulin
ginin turke, kamar yadda aka kawo cikin wannan nazari. A wajen tattara bayanai
an yi amfani da hanyoyi mabambanta kamar sauraren kaset-kaset na waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanƙwairo, musamman waɗanda aka nazarta, da kuma duba
littattafai da kundayen bincike da maƙalu da kuma tattaunawa da masana waƙoƙin
baka na Hausa domin samun bayanan da suka zama fitila ga nazarin. Daga ƙarshe
sakamakon bincike ya nuna cewa, Alhaji Musa Ɗanƙwairo
yana amfani da tubalan yabon mata a wasu waƙoƙinsa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.028
author/Fatima Ababakar Ɗanhassan
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |