Dabbobi Da Tsuntsaye Da Ƙwari a Matsayin Tubalan Gina Habaici a Waƙoƙin Haruna Aliyu Ningi

    Tsakure: 

    Waƙoƙin baka na Hausa, waƙoƙi ne da ake yaɗa manufofi da su ta fuskoki da dama. Mawaƙan baka na Hausa sukan isar da saƙonni ga alumma domin su wayar masu da kansu a kan abun da suke ganin za a iya cutar da su ko hannunka mai sanda a kan alamurran yau da kullum. Habaici, zambo ko baƙar magana hanya ce da mawaƙa ke bi domin su yi gugar zana ga wasu shuwagabanni ko masu sarauta domin su yi suka a cikin wasu al’amurra.Wannan takarda tana magana ne a kan habaici a cikin waƙoƙin siyasa wadda mawaƙi Haruna ningi ya yi ta “Katsinawa kar mu kyale shi”. . Manufar wannan muƙala ita ce domin a tsamo dabarun da mawaƙi Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da su wurin gina tubulin habaici a waƙar sa ta Katsinawa Kar Mu Kyale Shi.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.027

    author/Bashir Abu Sabe & Fatima Lawal Soja

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |