Yanayin Halayen Duniya a Wasu Waƙoƙin Adamu Ɗanmaraya Jos

    Tsakure: 

    Wannan maƙala ta gudana ne a kan wasu waƙoƙin makaɗa Adamu Ɗanmaraya Jos, wanda ya kasance makaɗi ne mai ɗabbaƙa al’adun al’ummarsa da kuma bibiyar yanayin rayuwarsu, da kuma irin yadda suke gudanar da ita a cikin duniya. Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu halaye da yanayi na rayuwar duniya a zubin ɗiyan waƙoƙin Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos. A yawancin waƙoƙinsa ya kan fito da saƙonni waɗanda suka dace da halayen rayuwar duniya ta nuna yadda zamantakewar al’umma ta ke. Wannan bincike an tsara shi ne bisa ra’in tsarin al’adu, wato, Cultural Schema Theory. An ƙirƙiri wannan ra'in ne a ƙarshen shekarar 1980s, waɗanda suka fara amfani da shi su ne, Naomi Quinn da masanin halayyar ɗan'adam Claudia Strauss. Ra’in ya bayyana cewa ana nazartar zamantakewar rayuwa da tunanin ɗan’adam a maganganunsa ko a cikin adabin da ya samar. Hakan ya sa aka yi amfani da wannan ra’i wajen nazartar tunanin Adamu Ɗanmaraya Jos game da duniya. Nazarin ya kafa hujja daga wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗin. Masana sun yi amfani da wannan ra’in wajen binciken tunanin mutane, musamman a fannin adabi irin su Kennedy (1994) da Pedersen (1994) da Houghton (2012) da sauransu. Haka kuma, an nemo misalan waƙoƙin ne daga kafar intanet da amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Gusau, (2019). A wannan maƙala an fahimci irin yadda Ɗanmaraya Jos ya fito da halin duniya da yanayin da take sanya mutane, musamman waɗanda suka ruɗu da ita, da kuma irin sauyin da ta ke yi wa mutane na ɗauka da ajiyewa. Har ila yau kuma, mawaƙin ya fayyace irin yadda duniya ta kasance mayaudariya, wadda ba ta da gwani. Haka kuma, an nuna cewa komai na duniya samamme ne kuma ƙararre, saboda haka duk abin da ke cikin duniya yana da lokaci, wata rana zai zama tarihi.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.026

    author/Alhassan Alhassan

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |