Tsakure:
Kore
da Ajawo sunansu ya sha bamban, amma da yawa idan aka nemi bayani game da su,
sai a ɗauko bayanin kore a ɗora
kan ajawo ko a ɗauko bayanin ajawo a ɗora
kan kore. Hakan ya nuna mafi yawan mutane bugu ɗaya suke yi masu. Domin nuna wa jama’a
cewa kowane bakin wuta da nasa hayaƙin,
wannan maƙala
za ta yi ƙoƙarin fito da abin ya bambanta kore da
ajawo ta fuskar ma’ana da sigoginsu. A ɓangaern tattara bayanai kuma bayan
nazarin gudunmuwar manazarta ta rubuce-rubucensu game da mau’du’in da ake
bincike a kai,
an kuma yi amfani da ziyarar gani da ido da hira da tattaunawa da masu
ruwa-da-tsaki game da waɗannan sana’o’in. Kore da ajawo dukansu a
bisa tafarkin wayo da dabara suke, saboda haka an ɗora
wannan maƙala
a bisa ra’in yaudara wanda wasu masana suka assasa (wato David J. Buller da
Judee K. Baurgoon a shekarar 1996). Wannan ra’i ya fito da hanyoyin da
mayaudara suke amfani da su domin su yi yaudara, kamar amfani da dabara da
wayo. ‘Yankore da ‘yan’ajawo duk suna amfani da waɗannan
hanyoyin. Binciken kuma zai yi magana akan wuraren da kore da ajawo suka
bambanta da kuma dalilin bambantarsu, sannan kuma a yi magana a kan inda suka
yi kama da juna. Sakamakon binciken zai fito da yadda ‘yankore da ‘yan’ajawo
suke gudanar da harƙallarsu
domin jama’a su kauce wa faɗawa tarkonsu.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.032
author/Buhari Lawali
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |