Kyauta a Bakin Makaɗan Baka Na Hausa: Nazari Daga Ɗiyan Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Waƙoƙin baka na Hausa suna taka muhimmiyar rawa a sassan rayuwar al’umma daban-daban. Su kuwa makaɗan baka mutane ne masu kaifin basira, kuma suke da hikimar sarrafa zance ta hanyar bayyana saƙonninsu ga jama’a, musamman abubuwan da suka shafi godiya da nuna jin daɗi a dalilin wani abin alheri da aka yi musu, kamar karimci da kyauta da sauransu. Burin wannan takarda shi ne, ta yi nazarin kyauta da wasu nau’o’inta a waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru wanda ya yi shuhura a fagen kiɗa da waƙa. Ta haka ne binciken ya bibiyi matanonin waƙoƙin mawaƙin, sannan a yi musu tarke na ilimi ta hanyar fito da yanaye-yanayen wasu kyaututtuka na karimci da girmamawa da ake yi wa makaɗan baka na Hausa a Bahaushiyar al’ada. An ɗora wannan bincike a bisa ra’in kwaɗaitarwa wanda yake sa a yi kyautatawa don jan ra’ayin wani kamar yadda Pratt (1980) ya yi nuni. Hanyoyin tattaro bayanai da aka yi amfani da su sun haɗa da; sauraren waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru a Memori da CD, sannan aka juyar da su a rubuce. An tattauna da masana da manazarta, kuma an bibiyi sawun wallafaffun littattafai da kundayen bincike da sauran maƙalu na ilimi. Binciken ya lura cewa, mutum yakan nuna farin cikinsa da jin daɗi idan an kyautata masa, kamar yadda tunanin makaɗa Sa’idu Faru ya yi nuna. Haka kuma, binciken ya fahimci cewa Hausawa suna ganin daraja da ƙimar makaɗan baka na Hausa, saboda haka ne ma suke yi musu tukuicin kyauta domin nuna gamsuwa da ayyukansu na kiɗa da waƙa.

    Fitilun Kalmomi: Kyauta, Makaɗa, Sa’idu Faru

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.033

    author/Muhammad Ammani, Ph.D & Aminu Babaji Adamu

    journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |