Ƙasar Hausa
Ƙasar
Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama, suna alaƙanta
ta da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na
duniya. Mu’azu (1993:1) ya bayyana ainihin ƙasar Hausa ta asali da “tana Afirka ta yamma ne,
a farfajiyar da ke tsakanin hamadar sahara da kuma dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun atlantika, watau daga kudu. Kuma ana
kiran ƙasar
da sunan Sudan ta yamma, watau tafkin Chadi da kuma gwiwar kogin Kwara a can
yamma.” A wani ƙaulin kuwa Dokaji, (1978) ya bayyana ƙasar
Hausa da ƙasa
ce da ta daɗe da wanzuwa a yammacin afirka wadda kuma ba a
iya haƙiƙance
lokacin fara wanzuwarta. A cewar wasu masana, ƙasar Hausa ita ce yankin nan na ƙasar
Sudan wanda ke wajen tsakiya- tsakiya. Daga gabas da ita akwai ƙasar
Borno, daga yamma ƙasar Dahomey (wacce yanzu ake kira jamhuriyar
Benin), daga arewa hamadar sahara, daga kudu kuma ƙasashen
da ake kira “Middlebelt”. Alhasan, (1982) Ya ce, asalin ƙasar
Hausa ya faro ne daga ƙauyukan Lalle da Asodu da ke arewa maso gabas da
Agadas can cikin ƙasar Nijar. Daga can Gobirawa suka taso kaɗan-kaɗan suka taru a muhallinsu na yanzu da ke cikin
arewacin Nijeriya.DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.031
author/Alh. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |