Tsakure: Saukar Alƙur’ani na farko ya zo shekarar (610 CE), ya ƙare shekarar (622CE). Alƙur’ani an saukar da shi ga Annabi Muhammadu (SAW) ta
hanyar Mala’ika Jibril. Da kalmar “Iqra” aka fara magana. Littafi ne da ke da
Surori (114) da aka kasa zuwa hizifi (60). Ayoyi 6,666, kalmomi 157,935 da
harufan da suka gina su 668,684; Allah Ka buwaya. Asalin harufan harshen
Larabci (28) ne. Daga cikinsu akwai harufu 15 marasa masu ɗigogi, guda 13
kuma masu ɗigogi. Harufa 7 ke da ɗigo ɗaya, 3 ɗigo biyu, 2 ɗigo uku.
Manyan wasula su ne “Alu Baƙi" da
“Alu Ja” sai “wasulan sama da ƙasa” da “damma
da shadda”. Waɗannan suke ba da damar karanta alƙur’ani ga kowa. A fassara Alƙur’ani cikin harsuna 114. A harsuna 47 kawai aka samu
wallafa shi cikakke. A fagen masana, an yi tafsiran Alƙur’ani 2,700, amma 300 kawai aka samu wallafawa. A cikin
harsunan Nijeriya kimanin 500, an fassara Alƙur’ani cikin fitattun harsuna cikin rubutun bokon
harshe, da ajamin harshe. Daga cikinsu akwai: Hausa, Yoruba, Kanuri, Fulfulde,
Nupe, Kyanganci da Igbo. A tarihance, Indiya ta fara taron gasar karatun
addinai fiye da shekara 100 da suka gabata, shekarar da aka gayyato Musulmi shi
ne ya zama zakara. Ta karatun Alƙur’ani an fara
ta a Indonesia a shekarar 1940, sai Malaysia (1961), Saudiya ta fara a 1980. A
zamanin da muke ciki (2024), Nijeriya ce gaba da yawan mahardata Alƙur’ani wanda Daular Borno ke jagoranta. Harshen da ya fi
harsunan Nijeriya ga fassara Alƙur’ani shi ne
Hausa. A Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta
fara tsara shi a Kabi a matsayin karo na 39. Akwai buƙatar saka Alƙur’ani cikin
tsarin koyarwa daga Firamare zuwa Jami’a, a ƙara fassara Alƙur’ani cikin
Harsunan Nijeriya domin tsaro da kyautata shugabanci.
Fitilun Kalmomi: Alƙur’ani, Musulunci, Ƙasar Hausa, Hausawa
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.005
author/Aliyu Muhammadu Bunza
journal/Tasambo JLLC 4(1) | May 2025 |