Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa da Al’adun Hausawa Kafin da Bayan Zuwan Turawa

    Tsakure: Tattalin arziki shi ne ƙashin bayan ci gaban kowace alumma a duniya. Ana iya gane ci gaban tattalin arzikin alumma ko koma-bayansa ta hanyar nazarin aladun wannan alumma. Haka kuma, adabi a mafi yawan lokaci yakan zama jagora na fahimtar alumma, halin da ta kasance a jiya da yau da kuma hasashen inda za ta samu kanta a ciki a gobe. Wannan maƙala mai suna:  ‘Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa da Aladun Hausawa Kafin da Bayan Zuwan Turawa’ ta ginu ne bisa manufar waiwayen hanyoyin bunƙasar tattalin arziki da ƙasar Hausa. An nazarci halin da tattalin arzikin ƙasar Hausa ya kasance, da tagomashin da baƙi suka yi wajen ci gaban tattalin arziki, da al’adu na neman arziki a ƙasar Hausa. An yi amfani da hanyoyin tattara bayanai daga litattafai da nazartar waƙoƙi da hira da masana tattalin arziki da al’ada. Har ila yau, an ɗora wannan aiki bisa ra’in sauyin al’adu wanda ya ginu a kan yadda al’adun al’ummomi suke sauyawa da abubuwan da suke haifar da sauyin. Sakamakon wannan bincike ya gano cewa Hausawa suna gina harsashin tattalin arzikinsu bisa kyawawan ɗabi’u na gaskiya da riƙon amana da taka-tsantsan. Haka kuma, an gano manyan sana’o’in gargajiya na Hausawa su ne farauta da noma da saƙa da rini da jima da sauransu, kuma dukkaninsu zamananci ya yi tasiri a kansu. A ƙarshe, an bayar da shawarar faɗakar da al’umma da a koma wa hanyoyin gargajiya da sana’o’in gargajiya da suka gina tattalin arzikinmu a baya domin samar wa al’umma mafita a kan halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa da talauci da rashin aikin yi.

    Titilun Kalmomi: Tattalin Arziki, Al’adun Hausawa, Ƙasar Hausa, Zuwan Turawa

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.004

    author/Dr. Hauwa Muhammad Bugaje

    journal/Tasambo JLLC 4(1) | May 2025 |